Nijer Ta Nemi Najeriya Ta Taimaka Don Warware Matsalar Karancin Makamashi

Kimani makonni biyu Kenan jumhuriyar Nijer ke fama da karancin man fetur a gidajen man kasar, wanda ya rage zirga-zirgan ababen hawa a duk fadin

Kimani makonni biyu Kenan jumhuriyar Nijer ke fama da karancin man fetur a gidajen man kasar, wanda ya rage zirga-zirgan ababen hawa a duk fadin kasar har da Yamai babban birnin kasar, har’ila yau ya shafi harkokin tattalin arzikin kasar.

Shafin yana labarai na yanar gizo IR News, ya bayyana cewa bayan da gwamnatin sojojin kasar ta kasa magance matsalar a cikin gida, ta tura wata tawaga karkashin jagorancin Ministan man fetur na kasar zuwa tarayyar Najeriya tare da bukatar ta aiko mata tataccen man fetur don magance matsalar.

Labarin ya kara da cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya dai tuni ta amince da bukatar, tare da bada umurnin a aikawa Jumhuriyar ta Niger tankunan man fetur har 300.

Wasu wadanda suka san al-amura a Jumhuriyar ta Niger sun bayyana cewa matsalar ta taso ne bayan da gwamnatin sojojin kasar suka sami matsala da kamfanin kasar China wanda yake haka da tashen man fetur a matatan mai ta Soraz, wanda ya kai da sojojin suka bukaci mutanen china su bar kasar.

JMI tana haka da sarrafa danyen man fetur tun shekara ta 2011, amma matsala tsakanin gwamnatin sojojin kasar da kasar China ta sa sun kasa samar da man da zai wadatar da kasar, ballanta na a yi maganar ganga 100,000 da kasar take son fara saida shi ga kasashen waje, ta hanyar bututun mai wanda zai bi ta kasar Benin zuwa kasuwannin duniya.

Juye-juyen mulkin da aka yi a yankin Sahel dai ya sa Jumhuriyar Nijar bata jituwa da kasashen kungiyar ECOWAS Wacce Najeriya take jagoranta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments