ministan harkokin wajen iran Abbas Araqchi da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Jodan Ayman safadi sun tattauna ta wayar tarho kuma sun jiddada cewa diplomsiya wata hanya ce ta tabbatar da zaman lafiya a yankin, duk da yake cewa Amurka na ci gaba da tara sojojinta a yankin tekun fasha da hakan ya kara jefa fargaba a fadin yankin.
tattaunawar ta waryar taro tsakanin Araqchi da Safadi ta zo ne a daidai lokacin da ake fargabar atisayin da Amurke ke yi a tekun fasha zai iya komawa rikici, da zai kara kawo rikici a hanyoyin diplomasiya a yankin. Araqchi ya sake jaddada kudurin iran na kare muradun kasar da kuma zama lafiya a yankin ta hanyoyin diplomasiya, yana mai nuna kokarin da Tehran ke yi na ganin an rage tashin hankali, sai dai Safadi ya nuna damuwa kan yadda tashin hankali zai iya yin illa a yankin baki daya , kuma ya jaddada goyon bayan jodan na yi amfani da diplomasiya a matsayin mafita mai inganci.