JMI Ta Bude Sabon Sansanin Sojojin Ruwa A Garin Jask Na Bakin Tekun Omman A Lardin Hurmozgan

Rundunar sojojin ruwa na JMI ta bude sansanin sojojin Ruwa mafi girma a kasar a garin Jask nab akin ruwa a lardin Huzmuzgan na kasar

Rundunar sojojin ruwa na JMI ta bude sansanin sojojin Ruwa mafi girma a kasar a garin Jask nab akin ruwa a lardin Huzmuzgan na kasar Iran kuma a bakin Tekun Umman.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa manya-manyan kwamandojojin sojojin kasar sun sami damar halartar bikin bude tashar jiragin ruwa kuma sansanin sojojin ruwa mafi girma a kasar.

Labarin ya kara da cewa. daga cikinsu akwai akwai Manjo Janar Muhammad Baghiri babban hafsan hafsojojin sojojin kasar da kumandan sojojin ruwa Admiral Shahram Irani da sauran manya-manyan jami’an sojojin ruwa na kasar.

Labarin ya kara da cewa sansanin sojojin ruwa na Jask yana kusa da mashigar ruwa ta Hurmus mai muhimmanci, ta inda dukkan jiragen ruwa wadanda suke fitowa ko shigowar tekub farasa ta nan ne suke wucewa.

Sansanin sojojin ruwa na Jask har’ilayu yana da matukar muhimmanci a fagen tsaron kasar Iran da kuma yanken tekun farisa da tekun amman da kuma ruwaye na yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments