Rahoto: Jirgin Hizbullah Maras Matuki Ya Samu Dakin Barcin Netanyahu Kai Tsaye

Wasu daga cikin hotunan da jami’an leken asiri na sojin Isra’ila suka amince a buga a wannan Talata, game da harin da Hizbullah ta kai

Wasu daga cikin hotunan da jami’an leken asiri na sojin Isra’ila suka amince a buga a wannan Talata, game da harin da Hizbullah ta kai a kan gidan Benjamin Netanyahu, sun nuna barna a wata taga mai dakuna da daya daga cikin jerin hare-haren da Hizbullah ta gudanar a ranar Asabar.

Wasu daga cikin tashoshin gwamnatin  haramtacciyar kasar Isra’ila ne suka watsa hotunan, duk kuwa da Isra’ila ta hana dukkanin kafofin yada labaranta daukar hotunan wurin da kuma watsa su.

Wannan yana zuwa nea  daidai lokacin da kungiyar Hizbullah ta samara  hukuamncea  kan cewa ita ce ta kaddamar da hari kan gidan Netanyahu.

Da dama daga cikin yahudawan sahyuniya masu sharhi kan harkokin siyasa da tsaro, sun yi imanin cewa, harin na Hizbullah ya zubar da tinkahon Isra’ila na nuna fifiko ta fuskar tsaro a dukkanin fadin gabas ta tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments