Jerin ‘Yan Takara 6 Da Zasu Fafata A Zaben Iran Na Ranar 28 Ga Watan Yuni 

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Iran ta sanar da sunayen ‘yan takara a zaben shugaban kasar mai zuwa a ranar 28 ga watan Yuni domin

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Iran ta sanar da sunayen ‘yan takara a zaben shugaban kasar mai zuwa a ranar 28 ga watan Yuni domin maye gurbin Shugaban mai rasuwa Shahid Ebrahim Ra’asi da ya rasu a hatsarin jirgin Helikwafta a tsakiyar watan Mayu da ya gabata tare da wasu mukarabansa.

Ga jerin ‘yan takarar da zasu fafata a zaben da dan takaitaccen tarihinsu

Mostafa Pourmohammadi, mai shekaru 64, ya rike mukamai daban-daban ya kuma rike mukamin minista a ma’aikatu daban daban.

Ya kasance Ministan Harkokin Cikin Gida daga 2005 zuwa 2008 da kuma Ministan Shari’a daga 2013 zuwa 2017.

Massoud Pezeshkian, mai shekaru 70, mai ra’ayin sauyi, ya kasance ministan lafiya daga shekara ta 2001 zuwa 2005 kuma dan majalisar wakilai daga yankin Tabriz tun shekara ta 2008.

Mohammad Baqer Qalibaf, mai shekaru 63, kakakin majalisar dokokin a Iran a yanzu, ya taba zama magajin birnin Tehran daga 2005 zuwa 2017.

Saeed Jalili, mai shekaru 59, babban malami, ya taba rike mukamin babban mai shiga tsakani kan batun shirin nukiliyar Iran, daga shekarar 2007 zuwa 2013, kuma ya kasance sakataren kwamitin koli na tsaron kasar daga shekarar 2007 zuwa 2013.

Alireza Zakani, mai shekaru 58, shugaban makaranta, magajin garin Tehran tun daga 2021, dan majalisa daga 2004 zuwa 2016 da kuma daga 2020 zuwa 2021.

AmirHossein Ghazizadeh Hashemi, mai shekaru 53, mai ra’ayin gurguzu, a halin yanzu shi ne shugaban gidauniyar shahidai da tsoffin sojoji.

 Ya kuma kasance dan majalisa daga 2008 zuwa 2021.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments