Ma’aikatar harkokin wajen Jamus ta la’anci harin da aka danganta ga Isra’ila kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a kudancin Gaza tare da yin kira da a gaggauta gudanar da bincike.
“Ba abin yarda ba ne ana kashe mutane yayin da suke neman mafaka a makarantu.
‘’Dole ne sojojin Isra’ila su daina kai hare-hare kan makarantu kuma a gaggauta gudanar da bincike,” in ji ma’aikatar a dandalin sada zumunta na X.
Bayanai sun ce Isra’ila ta kashe Falasdinawa 29 a harin da ta kai ta sama a wata makarantar da ‘yan gudun hijira suke samun mafaka a kudancin Gaza ranar Talata, a yayin da luguden wutar da dakatunta suke ci gaba yi a arewaci ya sa aka rufe asibitocin Birnin Gaza tare da tilasta wa mutane tserewa daga gidajensu domin neman mafaka.
Sojojin Isra’ila sun yi kisan kiyashi a makarantar Al-Awda da ke garin Abasan na gabashin Khan Younis, a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta fitar.
Bayanai sun ce an kai hari kan makarantu hudu a Gaza a cikin kwanaki hudu jere.