Jamus Ta Kammala Janye Sojojinta Daga Nijar 

Rukunin karshe na sojojin kasar Jamus ya fice daga Nijar kamar yadda kasar ta Jamus ta cimma yarjejeniya da hukumomin mulkin sojin kasar da suka bukaci su fice

Rukunin karshe na sojojin kasar Jamus ya fice daga Nijar kamar yadda kasar ta Jamus ta cimma yarjejeniya da hukumomin mulkin sojin kasar da suka bukaci su fice daga kasar kamar yadda ta kasance ga sojojin Faransa da na Amurka a watannin baya.

An yi bikn kawo karshen zaman sojojin ne a ranar 29 ga watan Agusta a sansanin jiragen sama na 101 da ke birnin Yamai tare da halartar jami’an rundunar sojan kasashen biyu.

A ranar 22 ga watan Disamba, 2023 ne, sojojin Faransa suka fice daga Nijar, wanda ya kawo karshen kasantuwar sojojin na faransa a yankin Sahel bayan korarsu daga Mali da Burkina faso.

Hakazalika, Amurka ta kammala janyewarta a farkon watan Agusta daga sansaninta na karshe a Agadas dake Nijar, inda gwamnatin kasar ta bukaci ta fice daga cikin watan Maris din da ya gabata.  

A watan Maris din shekarar 2024 ne Nijar ta kalubalanci yarjejeniyar soji dake tsakaninat da Amurka wadda ta bada damar kafa sansanin Amurka a arewacin kasar.

Ya zuwa karshen shekarar 2023, akwai kusan sojan Amurka 1,100 a Nijar, wadanda akasarinsu suna jibge a garin Agadas dake arewacin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments