Jam’iyyar Adawa Ta Ennahada Ta Tunusiya Ta Koka Kan Matsin Lamba Da Take Fuskanta

Jam’iyyar adawa ta Ennahada ta kasar Tunusiya ta sanar da cewa: Jami’an tsaron kasar sun kame shugabannin jam’iyyar a Tunisiya Jam’iyyar Ennahda Movement Party ta

Jam’iyyar adawa ta Ennahada ta kasar Tunusiya ta sanar da cewa: Jami’an tsaron kasar sun kame shugabannin jam’iyyar a Tunisiya

Jam’iyyar Ennahda Movement Party ta watsa rahoton cewa: Jami’an ‘yan sandan Tunusiya sun kama shugabannin kananan hukumomin jihar Ben Arous da ke yankin kudancin birnin Tunis fadar mulkin kasar, da Mohamed Al-Qalawi, mamba na ofishin zartarwar jam’iyyar da kuma Mohamed Ali Boukhatim, babban sakataren jam’iyyar na jihar Ben Arous.

A shafinta na Facebook, jam’iyyar ta Ennahda ta yi kira ga hukumomi da su hanzarta sako duk mutanen da ake tsare da su kan manufofi na siyasa, tare da dakatar da siyasar kame-kame da gudanar da shari’a kan ‘yan siyasa saboda kiyayya gare su, da kuma killace abokan hamayyar siyasa domin kuntata musu.

Jam’iyyar ta Ennahda ta dauki abin da ta bayyana a matsayin manufar kame a matsayin wani yunkuri na mahukuntan kasar na tada zaune tsaye a fagen siyasa da kuma kuntata wa ‘yan adawar siyasa, da nufin shirya zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 6 ga watan Oktoba cikin wani mummunan yanayi da zai karya himma da azamar ‘yan adawa a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments