Mataimakin babban kwamandan rundunar ‘yan sandan kasar Iran Birgediya Janar Qassem Reza’ei ya bayyana cewa: Akwai kyakkyawar alaka tsakanin al’ummar tsibirin Abu-Musa da jami’an tsaron kan iyaka da na ‘yan sanda, inda ya kara da cewa makiya suna kokari ta hanyar fitar da sanarwa maras tushe na neman tada fitina a tsibiran Iran guda uku, amma a kodayaushe sun gaza cimma munanan manufofinsu sakamakon wayewar kan al’ummun tsibiran da hadin kan jama’ar tsibiran uku da gwamnatin Iran.
Birgediya Janar Reza’ei ya kara da cewa: A ziyarar da ya kai tsibirin Abu-Musa ya tafi shiyar kudu mai nisa na yankin tsarkakke kuma mai kima mallakin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yayin da yankin ke ci gaba da kasancewa cikin tsaro da kwanciyar hankali na musamman, wanda ya kasance daya daga cikin mafi girman yanayin tsaro da aminci gami da hadin kai da kuma halartar jama’a a lokacin zaben shugaban kasa da aka gudanar a Iran a baya-bayan nan, kuma hakan alama ce ta inganci da kuzarin al’ummar wannan yanki.
Ya yi tsokaci kan yunkurin da wasu kasashe suke yi na kawo cikas ga zaman lafiyar da ake samu a wadannan tsibiran uku na tekun Farisa, yana mai cewa fitar da bayanai da dama da wasu kasashe suke yi, wadanda ba su da wata manufa face tada zaune tsaye a wannan yanki na kasar Iran, amma mummunar manufarsu ta kasa cimma nasara sakamakon hadin kan al’ummar tsibiran da goyon bayansu ga gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.