Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Allah Wadai Da Kutsen Sojojin Isra’ila A Cikin Kasar Siriya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da kutsen da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a kasar Siriya Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da kutsen da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a kasar Siriya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da shigar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila cikin yankin Julan na kasar Siriya, bayan mamaye wani yankin tsawon wasu shekaru a baya, tana mai jaddada wajibcin mutunta ‘yancin kasar Siriya da kuma imaninta cewa: Dole ne al’ummar Siriya su yanke shawara kan makomar kasarsu.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya fitar ya jaddada cewa: Wuce gona da iri kan kasar Siriya, a fili yake karara keta yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ne.

Ita ma kakakin gwamnatin Iran ta ce tana da imanin cewa: Al’ummar Siriya ne suke da hakkin yanke hukunci kan makomar kasarsu. Don haka ta jaddada wajibcin mutunta hurumin kasar ta Siriya, tana mai bayyana fatan cewa nan gaba kasar Siriya za ta zame alheri ga al’ummarta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments