Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi kakkausar suka kan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka ba bisa ka’ida ba a baya-bayan nan na gudanar da wani kamfen din kame wasu ‘yan kasar Iran da ke zaune a Amurka, tana mai bayyana irin mu’amalar da ake musu a matsayin babu dan Adamtaka a ciki.
Ali-reza Hashemi Raja, Darakta Janar mai kula da harkokin ‘yan gudun hijira na Iran a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Wannan kamen na zuwa ne a matsayin goyon bayan Amurka ga haramtacciyar kasar Isra’ila ta keta hurumin ‘yanci da yankin kasar Iran, yana mai jaddada cewa wadannan matakan sun saba wa ka’idojin da aka sani na dokokin kasa da kasa.
Hashemi Raja ya kara da cewa, rahotanni sun nuna cewa ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka (DHS) tare da hadin gwiwar hukumar kula da shige da fice da kuma kwastam (ICE) sun aiwatar da tsauraran matakai da tsare-tsare kan al’ummar Iran, ciki har da tsauraran matakan tsaro da fadada gudanarwa kan Iraniyawa lamarin da ya haifar da matukar damuwa ga iyalan Iraniyawa da ake tsare da su a Amurka.