Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Kebance Jiragen Saman Yaki Na Kai Hari Kan ‘Yan Sahayoniyya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta Sanar da cewa: Ma’aikatar tsaron kasar ta kebe jirgin saman maras matuki ciki kirar “Arash-2” da ta kera ne don

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta Sanar da cewa: Ma’aikatar tsaron kasar ta kebe jirgin saman maras matuki ciki kirar “Arash-2” da ta kera ne don kai hari kan haramtacciyar kasar Isra’ila

A ci gaba da gudanar ranakun atisayen soji domin ayyukan tsaron kasa, da sojojin Iran suke gwajin kai hare-hare da kuma sarrafa manyan na’urorin makaman tsaro a yankin da ke yammacin kasar, a karon farko sun nuna wasu jiragen saman yaki maras matuki ciki da aka kera a cikin gida masu tsnanin karfin munanan hare-hare irin na kunan bakin wake kirar “Ababil” da “Arash-2” da dakarun sojin kasar Iran zasu yi amfani da su wajen kare tsaron kasa duk lokacin da ya dace.

Jiragen saman “Ababil” ne suka jagoranci tawagar sabbin makaman, sannan wasu jiragen saman kunar bakin wake guda uku na “Arash” suka biyo bayansu, wadanda idan aka kai hari da su zasu tarwatsa wuraren da aka tura su.

Abin lura shi ne cewa: “jirgin Arash-2 yana ci nisan kilomita 2,000, wanda ya sa ya zama jagora a tsakanin takwarorinsa na jiragen saman yakin Iran da ma duniya baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments