Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Gwamnatin Siriya Da Al’ummar Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada goyon bayan kasarsa ga Siriya wajen yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada goyon bayan kasarsa ga Siriya wajen yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada a yayin wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na kasar Masar Badr Abdel Ati, manufofin Iran na goyon bayan gwamnatin Siriya da sojojinta da kuma al’ummar kasar wajen yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda.

A yayin tattaunawarsu a jiya Laraba, Araqchi ya bayyana sakamakon zantawar da ya yi da jami’an Siriya da Turkiyya a ziyarar da ya kai Damascus da Ankara.

Araqchi ya tattauna da ministan harkokin wajen Masar kan batutuwan da ke faruwa a yankin, tare da mai da hankali kan ci gaban da ke faruwa a Siriya.

Araqchi ya dauki matakin sake farfado da kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Siriya da kuma yaduwarsu a yankin a matsayin babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro a dukkan yankin, yana mai jaddada bukatar ci gaba da kokarin diflomasiyya da tuntuba tsakanin masu fada a ji a yankin don tunkarar wannan hatsari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments