Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Gargadi Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Da Wasu Kasashe

Iran ta gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da wasu kasashe Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’ar kasa

Iran ta gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da wasu kasashe

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’ar kasa da kasa Kazem Gharibabadi, ya gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA da wasu kasashen duniya kan ci gaba da bin tafarki maras kyau da suka yi a baya, yana mai jaddada cewa Iran za ta dauki natakin da ya dace daidai ayyukan da sauran bangarori suka dauka.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a na kasa da kasa ya mayar da martani a jiya Lahadi kan rahoton babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi kan wasu batutuwan kariya da suka shafi Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Wasu kafafen yada labarai sun wallafa wani bangare na cikakken rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, IAEA, Rafael Grossi, ya gabatar a jiya, wanda aka shirya gabatar da shi ga taron kwamitin gwamnonin dake tafe. Rahoton ya yi iƙirarin cewa yawan sinadarin Uranium da Iran ke da shi ya kai matakin da zai yi kusa da matakin da ake bukata wajen samar da makaman yaƙi kuma ya nuna rashin gamsuwarsa da Iran ke bayarwa duk da haɗin gwiwar da Iran ke yi da hukumar IAEA.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted