Jakadan MDD Ta Musamman A Kasar  Siriya Ya Yi Gargadin Kan Yiyuwar Wargajewar Al-Amura  AKasar Ta Siriya

Jakadan MDD Ta Musamman A Kasar Siriya Ya Yi Gargadin Kan Yiyuwar Wargajewar Al-Amura AKasar Ta SiriyaJakadan MDD Ta Musamman A Kasar Siriya Ya Yi

Jakadan MDD Ta Musamman A Kasar  Siriya Ya Yi Gargadin Kan Yiyuwar Wargajewar Al-Amura  AKasar Ta SiriyaJakadan MDD Ta Musamman A Kasar  Siriya Ya Yi Gargadin Kan Yiyuwar Wargajewar Al-Amura  AKasar Ta Siriya

Jakadan MDD na musamman a kasar Siriya Geir Pedersen ya bukaci kasashen duniya su yi sauri su taimakawa kasar Siriya kafin ma’aikatun gwamnatin kasar masu muhimmanci su kasa gudanar da ayyukansu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Pedersen ya na fadar haka a taron kasashen duniya don tattauna batun kasar ta Siriya a wani wurin shakatawa a kasar Jordan a yau Asabar.

Labarin ya kara da cewa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken, da manya–manyan jami’an diblomasiyyar na kasashen Turkiyya, Jordan da kungiyar Tarayyar Turai da kuma wasu kasashen Larabawa ne suka hadu don tattauna halin da kasar Siriya take ciki.

Jakadan MDD na musamman a kasar Siriya ya kara da cewa akwai bukatar a gaggauta kawo kayakin agaji zuwa kasar ta Siriya, sannan dole ne a gaggauta kafa zabebben gwamnati a kasar, wacce zata sami iko a duk fadin kasar saboda kada ta wargaje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments