Jakadan Iran A M D D Yayi Gargadin Cewa Iran Za ta Mayar Da Martani Mai Tsanani,Bayan Barazanar Da Trump Yayi Mata

rahotanni sun bayyana cewa jakadan kasar iran a majalisar dinkin duniya yayi gargadin cewa iran za ta mayar da martani mai karfi kan duk wani

rahotanni sun bayyana cewa jakadan kasar iran a majalisar dinkin duniya yayi gargadin cewa iran za ta mayar da martani mai karfi kan duk wani gigin kai mata hari daga bangaren Amurka, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soji kan kasar Iran.

a wani sako da ya aike da shi a shafinsa na X ya bayyana a ranar laraba cewa iran a shirye take a warware matsalar dake tsakaninta da Amurka ta hanyar Tattaunawa bisa mutuntua juna da kare maslahohi, to amma fa a shirye take ta kare kanta daga duk wani hari da za’a kai mata.

trump yayi  barazanar cewa idan iran ta kasa cimma wata matsaya da Amurka to za a kai mata harin soji, yace harin kuma zai yi matukar muni fiye da wanda ta kai kan cibiyoyin nukiliyarta a watan yuli da ya gabata

Iran ta harba makami mai linzami  kan sansanin sojin sama na Al Udeid dake Qatar, sansanin dake dauke da sojojin amurka masu yawa da kuma tarin kayan aikinsu, a matsayin martani kan hare-haren da Amurkan ta kai mata a cibiyoyinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted