Jakadan Iran A Riyadh Ya Godewa Saudiyya Saboda Yadda Ta Tsara Aikin Hajin Bana

Jakadan na Jamhuriyar musulunci ta  Iran a kasar Saudiyya Ali Riza Inayati ya fada wa jairdar ” Indpendent Arabiya” cewa:  Iraniyan da adadinsu ya kai

Jakadan na Jamhuriyar musulunci ta  Iran a kasar Saudiyya Ali Riza Inayati ya fada wa jairdar ” Indpendent Arabiya” cewa:  Iraniyan da adadinsu ya kai 90,000 sun yi aikin haji cikin sauki da nutsuwa a Makka, kamar kuma yadda su ka ziyarci masallacin manzon Allah (s.a.w) da makabartar Baki.

 Jakadan na jamhuriyar musulunci ta Iran a Saudiyyar ya kara da cewa; A halin yanzu mahajjatan na Iran suna cigaba da gudanar da sauran ayyuka domin kamala aikin hajin.

Ali Inayati ya kuma ce;  A matsayina na jami’in diplomasiyya na ga yadda hukumar Alhazai ta Iran da kuma ofishin wakilcin jagoran juyi su ka tsara aikin haji , kuma su ma mahukuntan Saudiyyar sun yi nasu kokarin da ya cancanci a yi musu godiya.

Inayati ya jaddada cewa; Iraniyawa suna cikin mahajjatan duniya da su ka fi gudanar da ayyukansu a cikin tsari, domin gabanin zuwa Saudiyya ana gudanar da tarukan wayar da kai da bayar da horo ga maniyyata.

Inayati ya kuma ce; A Tehran mahukunta suna daukar aikin haji a matsayin wata dama ta samar da hadin kai a tsakanin al’ummar musulmi da kuma kusantar Allah madaukakin sarki. Haka nan kuma yin tunani akan yadda za a warware matsalolin da suke addabar al’ummar musulmin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments