Jagoran ‘yan adawa da suka kwace mulki a kasar Siriya ya bayyana cewa: Ba zan amince a yi amfani da Siriya wajen kai hare-hare kan haramtacciyar kasar Isra’ila ba
Babban Kwamandan da ake kira da “Sashin Ayyukan Sojoji a Siriya” kuma tsohon jagoran ‘yan Adawan Siriya Ahmed Al-Shar’a (Al-Julani), ya tabbatar wa jaridar “The Times” ta kasar Birtaniya cewa: Ba zan yarda a yi amfani da Siriya a matsayin wajen kai hare-hare kan haramtacciyar kasar Isra’ila.
Al-Julani ya jaddada kudurinsa na karfafa yarjejeniyar kawo karshen yaki ta shekara ta 1974, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da cewa; Haramtacciyar kasar Isra’ila ma ta bi sahun kasarsa. Yana mai cewa: A shirye suke su mayar da masu sa ido na kasa da kasa, a kan iyakar Siriya da haramtacciyar kasar Isra’ila saboda ba su son wani rikici da haramtacciyar kasar Isra’ila ko kuma wani bangare na daban.
Al-Julani ya mayar da martani ga bayanin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi na ci gaba da kai wa yankunan Siriya hare-hare a matsayin matakin kariya don hana jibge ‘yan ta’adda a kan iyakokinta ba, inda ya ce: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta bukatar ci gaba da mamaye wadannan yankuna domin kare kanta saboda hambarar da gwamnatin Assad. ya kawar da barazanar da kungiyar Hizbullah da sauran mayakan sa-kai da Iran ke marawa baya.
Sannan Al-Julani ya yi kira ga gwamnatoci kamar Amurka da su cire sunan Hay’at Tahrir al-Sham daga cikin jerin ‘yan ta’adda, tare da cire mata duk wani takunkumi.