Jagoran ‘yan adawa a haramtacciyar kasare Isra’ila ya yi furuci da cewa: Shiyar arewacin Isra’ila na ci da wuta, kuma matakan tsaron yahudawa zasu rushe a shiyar
Jagoran ‘yan adawar Ya’ir Lapid ya kara da cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani shiri a nan gaba a Gaza, kuma ba ta da wani shiri na mayar da yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da suka tsere daga matsugunansu, don babu tsarin gudanar da aiki da bullo da dabarun fuskantar al’amura. Jagoran ‘yan adawar ya kara da cewa: Gwamnatin fira minista Netanyahu tana cike da rudu da rashin sanin makama.
A rubutun da ya yi a jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Yedioth Ahronoth ya bayyana cewa: Gobara tana ci gaba da habaka a gidajen yahudawan sahayoniyya a matsugunin Kiryat ta Arewa, da wata babbar gobara a yankin Ami’ad, kuma an rufe babbar hanyar zuwa arewa.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahita kasar Lebanon ce ta yi luguden wuta ta hanyar makamai masu linzami da kuma jiragen yaki marasa matuka ciki kan matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida a yankin Julan na kasar Siriya da aka mamaye da kuma yankin Galili, sannan gobarar tana ci gaba da ci a yankin tsaunin Rumim da ke Kiryat Shumona.