Search
Close this search box.

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Wajabcin Tallafawa Wadanda Ake Zalunta

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Daya daga cikin tabbatattun ayyuka a yau shi ne tallafawa wadanda ake zalunta a Gaza

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Daya daga cikin tabbatattun ayyuka a yau shi ne tallafawa wadanda ake zalunta a Gaza da Falastinu

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi kira da a kare martabar al’ummar musulmi, ya kuma jaddada muhimmancin hadin kan musulmi, yana mai cewa: Ba za a taba mantawa da batun al’ummar musulmi ba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a yau litinin, a lokacin da ya karbi bakwancin tawagar malamai, limaman Juma’a, da daraktocin makarantun mazhabar Sunna a duk fadin kasar, inda ya jaddada yin kira kan wajabcin kare mutuncin al’ummar musulmi.

Jagoran ya kuma jaddada muhimmancin kare fahimtar juna domin ci gaban Musulunci da hadin kan al’ummar musulmi da kuma dakile yunkurin masu son zuciya na neman gurbhata Musulunci, ya kuma ce: Batun hakikanin al’ummar musulmi lamari ne na asasi da ya wuce kishin kasa, da kuma iyakokin kasa. Don haka hakikanin al’ummar musulmi baya canzawa da tushensa.

Haka nan kuma ya yi nuni da yunkurin nuna kiyayya da nufin mayar da musulmi halin masu ko- in- kula game da matsayin Musulunci, ya kuma kara da cewa: Duk musulmin da ya yi biris da wahalhalun da wani musulmi yake ciki, ko a Gaza ko a wani bangare na duniya, ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments