Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Cewa Falasdinawa Suna Jihadi Don Allah Ne

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Al’ummar Falastinu da Gaza suna gwagwarmaya ne saboda Allah Madaukaki Jagoran juyin juya halin Musulunci

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Al’ummar Falastinu da Gaza suna gwagwarmaya ne saboda Allah Madaukaki

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa; Mujahidan Falastinu da Gaza suna gwagwarmaya ne saboda Allah Madaukaki. Jagoran yana mai jaddada cewa: Wajibi ne dukkanin musulmi su taimaka wajen dawo wa al’ummar Falasdinu da hakkokinsu na kafa ‘yantacciyar kasarsu da fadar mulkinta zata kasance Qudus kamar yadda kudurorin kasa da kasa suka tabbatar tare da mayar da Masallacin Al-Aqsa ga al’ummarta.

Jagoran ya yi nuni da cewa: Abin da ake gani a Gaza da Lebanon a yau kamar yadda ake gani ne a lokutan yaki, yana mai jaddada cewa: Wajibi ne kowa ya tallafa wajen kwato Masallacin Aqsa da ‘yantar da al’ummar Falasdinu daga kangi da hannun miyagun mutane masu zubar da jinin bil’Adama kananan yara da mata da kuma tsofaffi.

Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya jaddada cewa: Ita dai Amurka karya take yi na cewa: Ba ta tsoma baki a yakin Falasdinu da Gaza, amma nasara tana ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da                Hizbullahi kuma da yardan Allah karfin Hizbullah ya shige yadda da makiya suke tunanin murkushe ta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments