Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya karbi bakuncin zababben shugaban kasa Mas’ud Fizishkiyan, wanda ya lashe zaben da aka yi a ranar Juma’a.
A jiya Asabar ne dai jagoran juyin juya halin musuluncin na Iran ya taya zababben shugaban kasar ta Iran Ma’ud Fizishkiyan murnar cin zabe, tare da jinjinawa fitowar wadanda su ka kada kuri’a.
Har ila yau, jagoran juyin musulunci na Iran din ya kuma bayyana fatansa na ganin zababben shugaban kasar ta Iran ya yi aiki domin raya kasa da cigabanta, ta hanyar amfani da dammakin da ake da su.
Shi dai Mas’ud Fizishkiyan ya lashe zaben da aka yi ne a ranar Juma’ar da ta gabata bayan da ya sami kuri’u fiye da miliyan 16, da shi ne kaso 53.6% na jumillar kuri’un da aka kada.
Shi kuwa mai bi masa a baya Sa’id Jalili ya sami kuri’u miliyan 13 da ya kasance kaso 44.3%.