Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya ba da lambar yabo ta yaki ga Birgediya Janar Haji- Zadeh
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bai wa kwamandan sojojin sama na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Haji-zadeh lambar yabo.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya watsa rahoton cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bai wa kwamandan sojojin saman kasar na dakarun kare juyin juya halin Musulunci Birgediya Janar Ali Haji-zadeh lambar yabo.
An ba shi wannan lambar yabo ne bayan nasarar da harin mayar da martanin Iran kan haramtacciyar kasar Isra’ila na harin “Alkawarin Gaskiya” ya samu.
An zabi lambar karramawar ce a matsayin wata alama ta nasarorin da gwagwarmayar Musulunci da Sojoji suka samu a ayyuka daban-daban.
Ana ba da lambar yabon ne ga manyan jarumai na yaƙin da aka dora wa Iran wato -yaƙin Iran da Iraki- a shekara ta 1980 zuwa 1988) da shugabannin sojoji waɗanda suka gudanar da gagarumar hidima da ayyuka. Wannan lambar yabo tana da darajoji uku: lambar zinare, lambar azurfa da kuma lambar tagulla.