Jagoran juyin musulunci na kar iran Ayatullah sayyid Ali Khamna’i ya bayyana cewa kasar Amurka bata ji da dadi ba a yakin kwanaki 12 da ta kaddamar a kan kasar iran a watan yuni, duk da amafani da ta yi da manyan makaman yaki na zamani da suka hada da jiragen yaki da kuma makaman kariya .
Har ila yau jagoran yace Amurka da isra’ila sun sha kashi a yakin kwanaki 12 da suka kaddamar kan kasar iran, sun kai harin ne don su ci blus, sai suka koma da borin kunya, basu iya tabuka komai ba, wannan babban shan kashi ne a garesu,
Yace wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnatin sahyuniya ta shirya yakin shekaru 20, ta shirya tunzura mutane su juyawa tsarin musulunci na kasar baya, amma sai lamarin ya juya sabanin yadda suka yi tsammani, inda haka ya kara hadin kai tsakanin alummar kasar kuma reshe ya juye da mujiya.
Yace a ranar 13 ga watan yuni Amurka ta kaddamar da harin tsokana kan kasar iran inda ta kashe manyan jami’an sojin kasar da masana fasahar nukiliya da ma sauran fararen hula. Sai dai iran ta mayar da martani kan wasu sansanoninta dake yankin da suka hada da sansaninta na Al-udeida na kasar Qatar wanda shi ne mafi girma a yammacin asiya.