Search
Close this search box.

Jagora: Wakokin Farisanci Sun Yi Tasiri Mai Girma A Zamanin Yaki

A yayin da ya gana da mawaka da kuma sauran ma’abota adabin Farisanci a darejn jiya  Talata, jagoran juyin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya

A yayin da ya gana da mawaka da kuma sauran ma’abota adabin Farisanci a darejn jiya  Talata, jagoran juyin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana gamsuwarsa akan yadda adabin Farisanci yake cigaba a bunkasa kuma ya yi iashara da yadda a zamanin kallafaffen ya zama mai dauke da muhimman sakwanni masu tasiri.

Sayyid Ali Khamnei ya kuma yi kira da a cigaba da amfani da adabin na Farisanci a fagagen aikewa  duniya sakwannin da suke cikinsa na addini,cigaba, jajurcewa da kuma jarunta.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana cewa;sharadin yin tasiri  ta fuskar adabi, yana kunshe da zabar nau’in sakwannin da za a aike, kuma wajibi ne wadannan sakwannin su kasance na addini da kyawawan halaye da cigaba sannan kuma da nuna fuskarsa ta Iran.

Jagoran juyin juya halin musuluncin ya kuma amabci jajurcewa, jaruntar al’ummar Iran wajen fada da zalunci da masu wuce gona da iri na duniya da Amurka da ‘yan sahayoniya suke wakilta a matsayin irin wadannan sakwannin da za a aike wa duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments