Falasdinawa fiye da dubu 45 suka gudanar da sallar Juma’a a masallacin Al-Aksa a jiya jumma’a duk da hana matasa da damaa shiga masallacin wanda sojojin HKI su ka yi.
Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya kara da cewa sojojin yahudawan sun hana matasa Falasdinawa da dama shiga masallacin, sun kuma kama matasa da dama wadanda suka nuna rashin amince masu shiga masallacin.
Rahotanni da suke fitowa daga HKI sun bayyana cewa sojojin yahudawan sun sanya shinge na karafa a kofofin shiga farfajiyar masallacin, kuma banda haka hana matasa shiga masallacin, sun kuma kama wasu daga cikinsu sun tafiya da su.
Gbanin hakan dai sojojin yahudawan sun bada dama da kuma kariya ga yahudawan sahayoniyya don gudanar da ayyukansu na ibada ta Talmud a cikin farfajiyar masallacin sun kuma ci gaba da kare su daga Falasdinawa.