Wani rahotu na musamman dangane da yaki A Gaza, hukumar kare hakkin bil’adma na MDD mai kula da al-amuran Falasdinawa ya bayyana cewa dole ne a tsaida yaki a gaza, a kuma dorawa HKI takunkuman tattalin arziki sannan a kare al-ummar falasdinawa daga cutarwar yahudawan.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na daliban jami’a a nan Iran ya nakalto Francesca Albanese dan rahoton na musamman kan al-amuran take hakkin bil’adama a hukumar yana fadar haka a wani rahoton da ya fitar.
Albanese ya kara da cewa hukuncin da kotun kasa da kasa ta ICJ ta fitar a cikin watanin da suka gabata dangane da hana HKI kisan kare dangi a Gaza, bai yi wani amfani ba. Ya kuma kara da cewa, saboda haka dole ne kasashen duniya su dorawa HKI takunkuman tattalin arziki.
Rahoton ya kara da cewa halin da al-ummar Falasdinu a Gaza suke ci baa bin siffantawa ba, kuma al-ummar Falasdinu suna cikin wani mummunan halin da mutum ba zai iya sawwara shi ba. Kuma al-amarin yana da ban tsoro. Sannan ya kammala da cewa dole ne MDD ta aikata abinda ya hau kanta na samarwa falasdinawa yan gudun hijira a gaza aminci.