Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa Iran ta yi hasarar abin da ya kira ‘yan amshin shata a yankin yammacin Asiya, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta da wasu rundunoni masu wakiltarta a yankin”.
“Wasu a kullum suna cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi asarar dakarunta a yankin, Wannan ba gaskia ne ba inji.
“’Yan Yemen na yaki ne bil hakki; Hizbullah ma haka; Hamas da Jihadi Islami kuma suna yaki ne don an tilasta musu yin haka, wanda ya sanya basa yin aiki a madadinmu.”
Yayin da yake jaddada matsayin Iran, Jagoran ya jaddada ikon kasar na gudanar da ayyukanta cikin ‘yancin kai idan har ya zama dole. “Idan har muka yanke shawarar yin hakan, ba ma bukatar wakilai,” in ji shi.
Har ila yau Ayatullah Khamenei ya tabo halin da ake ciki a kasar Siriya, inda ya bayyana kyakkyawan fata ga kasar duk kuwa da kalubalen da ake fuskanta.