Italiya : Mutane da dama sun jikkata yayin arangama da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu 

A Italiya mutane da dama sun jikkata yayin arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Rahotanni sun ce kimanin mutane 10 ne

A Italiya mutane da dama sun jikkata yayin arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.

Rahotanni sun ce kimanin mutane 10 ne suka jikkata yayin zanga-zangar ta nuna goyon bayan Falasdinu bayan da ‘yan sanda suka yi kokarin hana masu zanga-zangar da ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye a ranar Asabar.

Zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu, wacce ta fara ranar Juma’a a Rome, Milan, Naples, da Bologna, ta bazu a ranar Asabar zuwa Florence, Pisa, Ancona, Trieste, Bari, da Alessandria.

Zanga-zangar ta nuna goyon baya ga Gaza da al’ummar Palasdinu na karuwa a tashoshin jiragen ruwa, jami’o’i, makarantu, da wuraren taruwar jama’a a Italiya gabanin zanga-zangar kasa da aka shirya yi a ranar 4 ga Oktoba a birnin Rome.

A ranar 22 ga watan Satumba, an gudanar da wani yajin aikin gama-gari na sa’o’i 24 da kungiyoyin kwadago da dama suka kira a fadin kasar Italiya domin nuna adawa da hadin kan kasar a kisan kiyashin da aka yi a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments