Isra’ila : ‘Yan adawa sun kira zanga-zangar gama-gari bayan korar shugaban Shin Bet

Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da

Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa  na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.

 Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv cewa “Idan har gwamnatin 7 ga watan Oktoba ta yanke shawarar kin yin biyayya ga hukuncin kotun, to za ta zama haramtacciyar gwamnati a wannan rana.”

“Dole ne tattalin arzikin kasar ya tsaya cik, majalisa ta shiga yajin aiki, kotu ta shiga yajin aiki, hukumomi su shiga yajin aikin, ba jami’o’i kadai ba, har da makarantu.” Inji shi.

A ranar Juma’a ne Kotun kolin Isra’ila ta dakatar da matakin da gwamnati ta dauka na korar shugaban Shin Bet, Ronen Bar, wanda ba a taba ganin irinsa ba, wanda sanarwar korar tasa ta sake haifar da baraka a tsakanin al’umma.

Amma Netanyahu ya dage kan cewa,”Ronen Bar ba zai ci gaba da zama shugaban Shin Bet ba, ba za a yi yakin basasa ba, kuma Isra’ila za ta ci gaba da kasancewa a matsayin kasa ta dimokuradiyya,” in ji shi a cikin wani sakon bidiyo inda yake kalubalantar Kotun Koli.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments