Isra’ila Ta Umurci Sojoji Su Shirya Tsarin Fitar Da Faladinawa Daga Gaza

Ministan tsaron Isra’ila, Isra’ila Katz ya umarci sojojin gwamnatin kasar da su shirya wani shiri na “ficewar” Falasdinawa daga zirin Gaza. Umarnin Katz ya biyo

Ministan tsaron Isra’ila, Isra’ila Katz ya umarci sojojin gwamnatin kasar da su shirya wani shiri na “ficewar” Falasdinawa daga zirin Gaza.

Umarnin Katz ya biyo bayan shawarar Shugaba Donald Trump na tilastawa Falasdinawa Gaza barin zirin da kuma sanya Amurka ta mamaye yankin da yaki ya lalata.

“Na umurci IDF da su shirya wani shiri don ba da damar ficewa na radin kan mazauna Gaza,” in ji kakakin na Isra’ila a cikin wata sanarwa.

Katz ya bayyana cewa ya fadawa sojojin Isra’ila da su yi shirin da “zai ba da damar duk wani mazaunin Gaza da ke son barin yankin zuwa, ga duk wata kasa da yake son karba.”

Ministan tsaron Isra’ila ya kara da cewa “Tsarin zai hada da zabin fita ta kasa, da kuma shirye-shirye na musamman na jiragan sama da kuma na ruwa.”

Katz ya ce yana maraba da “tsarin da Trump ya dauka, wanda zai iya baiwa wani kaso mai yawa na al’ummar Gaza damar yin kaura zuwa wurare daban-daban na duniya.”

A wani labarin kuma kungiyar Hamas ta bukaci da a gudanar da taron gaggawa na kasashen Larabawa domin mayar da martani ga shawarar da shugaba Donald Trump ya gabatar na mamaye yankin Falasdinu da kuma korar al’ummar kasar.

 A cikin wata sanarwa da kakakin Hamas Hazem Qassem ya fitar, ya ce “Muna kira da a gudanar da taron gaggawa na kasashen Larabawa don tunkarar shirin korar Palasdinawa daga Gaza, inda ya bukaci kasashen Larabawa da su bijirewa matsin lambar Trump, su kuma jajirce,” yayin da ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki kwararan matakai kan shirin na Trump.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments