Sojojin Isra’ila sun umarci mazauna Khan Younis su yi hijira daga unguwar Al Jalaa wanda a baya wuri ne da sojojin suka ayyana a matsayin “yanki mai aminci”.
Unguwar Al-Jalaa ba za ta ci gaba da kasancewa a matsayin “wuri mai aminci ba,” in ji sanarwar sojojin.
Ta yi iƙirarin cewa mayaƙan Hamas na “aiki” daga unguwar tare da cewa wurin zai kasance “wuri mai hatsari na yaƙi.”
Duk da cewa a baya sojojin Isra’ila sun rinƙa ayyana wasu wuraren a matsayin “masu aminci,” amma suna ci gaba da kai munanan hare-hare a wuraren tare da jawo mutuwar Falasɗinawa da dama.