Search
Close this search box.

Isra’ila ta kara kashe wani adadi mai yawa na Falastinawa fararen hula a Gaza

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa da dama a harin da ta kai ta sama a wani gida da ke arewacin Gaza, a cewar Hukumar Tsaron fararen-hula

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa da dama a harin da ta kai ta sama a wani gida da ke arewacin Gaza, a cewar Hukumar Tsaron fararen-hula ta yankin.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce tawagarta ta gano gawawwaki bayan wani jirgin yaƙin Isra’ila ya kai hari a gidan iyalan Al Hajin da ke Jabalia.

Harin ya lalata gidan da ma wasu gidaje da ke yankin, a cewar wani ganau.

Tawagar hukumar tsaron da mazauna yankin na ci gaba da tona ɓaraguzai suna neman mutanen da gine-ginen suka danne.

Tun da farko, hukumar ta ce hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai a wasu yankunan Birnin Gaza sun yi sanadin mutuwar gomman Falasɗinawa tare da jikkata wasu da dama.

“Mutane da dama sun yi shahada, wasu sun jikkata sannan gine-gine sun danne wasu a yankunan al-Daraj, Tuffah da Tsohon City sakamakon hare-haren bamabamai na rashin hankali da sojojin mamaya suka kai waɗannan yankuna,” in ji Mahmoud Basal, mai magana da yawun hukumar, a wata sanarwa da ya fitar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments