Jaridar “Isra’ila Home” ta buga rahoton da yake cewa Tel Aviv ta fara tattauna hanyar da za a kafa kwamitin na kasa da kasa wanda zai karkatsa Syria zuwa kananan kasashe.
Jaridar ta ce ana yin wannan tattaunawar ne a asirce amma kuma da akwai jin tsoron cewa watakila wannan tunanin ba zai sami karbuwa ba a tsakanin mutanen Syria.
Har ila yau wannan rahoton ya ce an yi wannan tattaunawar ne a tsakanin ministan harkokin tsaron Yisra’il Kats da wasu tsirarun mutane.
Har ila yau wani sashen na rahoton ya ce, Isra’ila ba tad a niyyar cigaba da zama a cikin kasar Syria,amma kuma a lokaci daya ba za ta fita daga ciki ba a cikin gajeren lokaci a nan gaba, har sai an sami daidaituwar al’amurra a cikin Syria.
Anan gaba ana sa ran cewa wannan tattaunawar da minstan tsaro yake jagoranta ta za hada da Fira minista, tare da mayar da hankali akan shigar Turkiya cikin kasar Syria.
Al’ummun Kurdawa da kuma Duruz ne dai Isra’ilan take son mayar da hankali wajen ganin ta fitar da su daga Syria da mayar da su kasashe masu zaman kansu.
Tun bayan faduwar gwamnatin Basshar Asad ne dai Isra’ilan take kai wa Syria hare-hare masu tsanani tare da lalata kusan dukkanin makamanin kasar.