Jakadan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran a MDD, Amir Sa’id Iruni ya bayyana cewa; Idan har Isra’ila ta kai wa Iran wani harin,to za ta fuskanci mayar da martani mai tsanani.
Jakadan na Iran a MDD ya kuma ce, harin na Iran halartaccen martani ne akan harin da Isra’ila ta kai wa karamin ofishin jakadancinta a birnin Damascuss na kasar Syria.