IRGC: Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya Zasu Kori Amurka Da HKI Daga Yankinsu nan Gaba

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ta bayyana cewa kawancen masu gwagwarmaya a yankin Asiya ta kudu zasu kara fadada gwagwarmayansu har

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ta bayyana cewa kawancen masu gwagwarmaya a yankin Asiya ta kudu zasu kara fadada gwagwarmayansu har sai ya kaiga kasashen yankin zasu kori sojojin Amurka da HKI daga yankin.

Kamfanin dillancin laraban Tasnim na kasar Iran ya nakalto IRGC suna fadar haka a dai dai ranakun tunawa da fara dawowan fursinonin kasar Iran daga Iraki bayan yakin shekaru 8 da kasar. A shekara 1990 zuwa sama.

Labarin ya kara da cewa kwancin masu gwagwarmaya a yankin zasu kara fadada har zuwa sauran kasashen yankin inda zasu kai ga korar sojojin Amurka da yankin.

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a na kasar Iran sun bayyana cewa akwai lokacin da zai zo inda kasashen musulmi zasu sami cikekken iko a kan kasshensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted