Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya bayyana cewa karfin sojojin kasarsa ya wace kan iyakokin kasar, don haka ya gargari makiyan kasar, su dai-daita kansu da irin karfin da zasu kara da shi, idan sun takaleshi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Hussain Salami ya na fadar haka a wani bikin da aka gudanar a kan jirhin ruwan yaki mai suna ‘shahid Rudaki’ kusa da birnin Bandar Abbas dake bakin taku farisa a jiya litinin.
Janar Salami ya kara da cewa, idan makiyammu basu yi haka ba, to mai yuwa kuskurensu na farko zai zama kuskurensu na karshe.
Yace babu wani karfi da kai karfin sojojin JMI ta sama, ta kasa ko kuma ta ruwa. Janar Salami ya kuma yaba da sadaukarwan da sojojin kasar suka yi a bayan da kuma wanda suke ci gaba da yi, a cikin gida ko a fagen fama.
A wani wuri a jawabinda Janar Salami ya kara da cewa gwamnatin JMI tana taimakawa kawayenta a yankin, amma kuma ko wannensu yana kera makamansa da kansa ne, kamar yadda muma muke kera makamammu da kammu. Babu wanda yake dogaro da wani a tsakanimmu.