Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran ta ce kasar za ta zabi lokacin da ya dace ma ta domin mayar da martani kan kisan da aka yi wa tsohon shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Tehran, wanda kuma zai sanya Isra’ila cikin rudani.
Birgediya Janar Ali Mohammad Naeini, mai magana da yawun rundinar ta IRGC kuma mataimakin shugaban sashen hulda da jama’a ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a ranar Talata.
Ya ce mai yiwuwa martanin Iran ba lallai ba ne ya zama maimaicin irin wanda ya gabata a kan gwamnatin Isra’ila ba.
An kashe Haniyeh da daya daga cikin masu tsaron lafiyarsa a Tehran a ranar 31 ga watan Yuli, kwana guda bayan da ya halarci bikin rantsar da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian.
Bayan kisan gillar, IRGC ta bayyana cewa Haniyeh ya yi shahada ne ta hanyar wani makami mai linzami da aka harba daga wajen gidansa da ke Tehran.