Babban mai bawa shugaban rundunar IRGC a nan Iran ya ce yakamata Amurka ta kawo karshen yakin da take yi da Iran, don ta yi duk abinda zata yi a cikin watanni kimani 7 da suka gabata bata sami nasara a kan Iran ba.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakaltp Burgediya Janar Mohammad Naqadi yana fadar haka a nan Tehran, ya kuma kara da cewa, daga ranar 28 ga watan Fabrayru na wannan shekarar zuwa 7 ga watan Afrilu Amurka ta yi amfani da dukkan karfinta wajen yakar JMI amma ta kasa yin haka. Don haka dole ne ta kawo karshen wannan yakin sai dai idan tana son kashe kai.
Janar Naqadi ya ce, Iran ta yi amfani da kasha daya % na yawan makaman da Amurka take da su ta kuma sami nasara a kanta, haka kuma ance HKI ce na hudu a karfin makamai a duniya, amma sun kasa samun nasara kan JMI a fafatwa na watanni kimani 7 da suka gabata, don haka lokaci yayi da yakamata su kawo karshen wannan yakin.
Janar Naqadi ya ce wasikar da IRGC ta rubutawa mutanen Amurka ta maida hankali ne ga dalilanda suka sa Amurka da HKI suka kasa samun nasara a kan JMI a yakin da suka dorawa kasar. Ta kuma Bawa Amurkawa shawara kan abinda yakamata su yi da shuwagabanninsu yan siyasa.