Jakadan kasar Iran a MDD ya bayyana cewa kasarsa zata ci gaba da goyon bayan mutane da gwamnatin kasar Siriya kan yan ta’adda da kuma matsalolin tattalin arzikin da kuma mamayar da wasu kasashe sukewa kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Amir Saeed Iravani jakadan kasar Iran a MDD yana fadar haka, a wani zaman kwamitin tsaro na majalisar a ranar litinin da ta gabata.
Iranvani ya kara da cewa, gwamnatin HKI tana kai hare hare kan kasashen yankin, wadanda suka hada da Falasdinu Yemen a kwanan nan da kuma kasar Siriya amma kwamitin tsaro na majalisar ya kasa yin koma.
Irawani ya zargi kasar Amurka da mamayar wasu yankuna na kasar Siriya da kuma zama barazana ga kasar da kuma kasashen yankin da dama, sannan a wani lokaci takan dorawa kasar Iran alhakin dukkan abinda yake faruwa a yankin.
Iravani ya kamala da cewa gwamnatin Iran tana allawadi da samuwar sojojin Amurka kan kasar Siriya ba tare da amincewar gwamnatin kasar ba, da kuma hare haren da HKI take kaiwa kan wurare daban daban na kasar Siriya a duk lokacinda taga damar hakan.