Iran: Za Mu Baje Muhimman Cibiyoyin  HKI Da Kasa

Jami’in dakarun kare juyin musulunci na Iran janar Ibrahim Jabbari ya gargadi HKI da cewa, idan har ta kawo wa Iran hari, to shakka babu

Jami’in   dakarun kare juyin musulunci na Iran janar Ibrahim Jabbari ya gargadi HKI da cewa, idan har ta kawo wa Iran hari, to shakka babu Iran din za ta mayar da martani, ta kuma baje wasu muhimman cibiyoyinta da kasa.

 Janar Ibrahim Jabbari, wanda shi ne mai bai wa kwamandan dakarun kare juyin musulunci shawar, ya kuma ce, Amurka ce take daure wa HKI a dukkanin laifukan da take aikawa a Gaza da kuma Yemen, amma ba su isa su shelanta yaki akan Iran ba, domin sojojinmu suna cikin shirin ko-ta-kwana.

Janar din na Iran ya kuma ce; Idan har aka kawo wa kasarmu hari, to kuwa za mu baje kamfanoni da muhimman kamfanoni na ‘yan sahayoniya da kasa.

Da yake Magana akan kungiyoyin gwgawarmaya, janar Ibrahim Jabbari ya ce; Dakarun Hamas, da Hizbullah suna nan da karfinsu.

 Dama tun a jiya Talata ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqci ya bayyana cewa; Iran za ta mayar da martani akan duk wani hari da ‘yan sahayoniya za su kawo mata.

Arqchi ya kuma ce; “makiyanmu sun san cewa babu wani lungu da sako da makamanmu masu linzami ba za su isa ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments