Iran Tana Samun Ci Gaba A Kera Makaman Kariya Kafada-Da-Kafada Da Kyautata Makamanta Masu Linzami Da Kuma Jiragen ‘Drones”

Wani babban Jami’in soje na kasar Iran ya yabawa masana fasahar kera makamai na kasarsa saboda ayyukan ci gaban da suka samar a cikin gida

Wani babban Jami’in soje na kasar Iran ya yabawa masana fasahar kera makamai na kasarsa saboda ayyukan ci gaban da suka samar a cikin gida wanda ya bawa kasar damar wadatuwa daga neman wasu makaman daga kasashen waje. Musamman makaman ‘Drones’ ko jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, wadanda kuma, JMI ta shahara da su.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto Burgediya Janar Ali Shadmani mataimakin shugaban cibiyar rundunar Khatamul Anbiya yana fadar haka a  kasuwar baje kolin fasahar kayakin yaki ta shekara ta 2024, wanda ke gudana a halin yanzu a lambun ‘Patriot’ da ke birnin Mosco na kasar Rasha.

Janar Shadman ya kara da cewa: Duk wanda ya zo bangaremmu yana sha’awar ganin jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa wadanda muka shahara da su a duniya, har’ila yau da makamai masu linzamu da muke samarwa 100% daga cikin gida.

Shadmani Ya kamala da cewa masana’antun makaman kasar Iran sun sami ci gaba mai yawa a shekarun da suka gabata a bangarori daban-daban, wadanda suka hada da bangaren yake-yaken yanar gizo da tsare-tsaren yaki a sararin samaniya da kuma cikin ruwa. Banda haka ta sami ci gaba a bangaren sadawar, fasahar AI (Artificial intelligent) da sauransu.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments