A cigaba da siyasarta ta kin jinin Iran, Baitulmalin Amurka ya sanar da kakaba sabon takunkumi akan wasu mutane 3 na Iran da kuma wasu cibiyoyi 4.
A cikin shekaru 40 na bayan nan dai Amurkan ta mayar da kakabawa Iran takunkumi zuwa wani salon yakin tattalin arziki da take yi daga lokaci zuwa lokaci, wanda yake shafar bangarori mabanbanta na soja, siyasa da jami’an diplomasiyya.
Takunkuman na Amurka dai ba su hana Iran cigaba da ayyukanta na raya kasa da cigaba ba.