Iran Ta Yi Kira Ga Kasashen Larabawa Na GCC Su Maida Hankali Wajen Dakatar Da Yaki A Gaza Maimakon Zargin Iran Da Abubuwan Da Basa Da Tushe

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibof ya yi kira ga kasashen larabawa na yankin tekun farisa GCC da su maida hankali kan tsaida

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibof ya yi kira ga kasashen larabawa na yankin tekun farisa GCC da su maida hankali kan tsaida yakin da ke faruwa a yankin maimakon bata lokacindasu wajen zargin Iran da kwace  tsibiransu guda uku a cikin tekun farisa, kamar yadda yazo cikin jawabin bayan taronsu da kasashen turai a birnin Brussels na kasar Belgium a jiya Asabar.

Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana haka a ne a yau Lahadi a lokacinda ya ke bude zaman majalisar dokokin kasar ta yau a nan birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa batun tsabiran Iran uku da suke ta Magana a kansu abu ne wanda ba za su taba samu ba, kuma suna bata lokacinsu ne kawai.

Qalibof ya gargadi kasashen Turai dangane da goyon bayan da suke bawa HKI tare da taimaka mata da makamai don ta ci gaba da kissan kiyashin da take yi a Gaza.

Ya ce tsibiran Tembe kuchek da tumbe bozorg da Abu musa, tsibirai ne wadanda babu wanda ya isa ya rabasu da Iran.

Jakadan kasar Iran a MDD ma ya yi allawadai da tarayyar turai EU da kuma kasashen GCC don matsayin da suka dauka kan Iran ba tare da binciken da ya dace ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments