Iran Ta Yi Allah Wadai Da Kai Harin Kan Masu Ziyarar Imam Husain Jikan Manzon Allah A Afganistan

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai wa maziyarta Karbala na kasar Afganistan Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai wa maziyarta Karbala na kasar Afganistan

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasir Kan’ani ya yi Allah wadai da harin da kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS ta kai kan jama’ar da suka zo tarbar maziyartan da suka dawo daga birnin karbar bayan ziyarar           hubbaren jikan Manzon Allah Imam Husaini {a.s} a karbala mai alfarma.

Kan’ani ya jajantawa shahidan harin ta’addancin da aka kaiwa tawagar masu tarbar maziyartan Imam Husaini {a.s}, wadanda suka dawo daga Karbala mai alfarma a lardin Ghor na kasar Afganistan, yana mai rokon Allah Madaukakin Sarki da ya gaggauta dawo da sauki ga wadanda suka jikkata. Ya kuma yi kakkausar suka ga wannan aiki zalunci na rashin zurfin tunani da ke dauke da rashin dan Adamataka, wanda kungiyar ta’addanci ta ISIS ta dauki alhakinsa.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS a Afganistan ta dauki alhakin harin da aka kai kan fararen hula a tsakiyar kasar. Yayin da gwamnatin Taliban ta sanar da mutuwar fararen hula ta hanyar harbinsu bindiga.

Kungiyar ISIS ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar a tasharta ta Telegram cewa mambobinta sun kashe ‘yan Shi’a 15 tare da raunata wasu 6 na daban a wani hari da suka kai a tsakiyar Afghanistan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments