Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sake Neman Zaman Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukiliyarta

Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martini kan batun neman sake sabon zaman tattaunawa kan Shirin makamashin nukiliyar Iran Ministan harkokin wajen kasar Iran

Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martini kan batun neman sake sabon zaman tattaunawa kan Shirin makamashin nukiliyar Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa ko za a sake gudanar da wani sabon zaman tattaunawa kan Shirin makamashin nukiliyar Iran ko kuma a’a, hakan ya dogara ne kan shirye-shiryen da daya bangaren ke yi, yana mai cewa: A shirye Iran take ta gudanar da zaman tattaunawa a bisa tubalin gaskiya da mutunci da zasu tabbatar da hakkin al’ummar Iran tare da la’akari da kiyaye jajayen layukan da Iran ta gindaya.

A wata hira da manema labarai da ya gudanar a jiya Laraba dangane da zagayowar ranar shahadar shugaban nasara, Araqchi ya bayyana cewa: Idan ba don karfin Iran na makamai masu linzami ba, da babu wanda zai nemi tattaunawa da ita.

Dangane da matsayin ma’aikatar harkokin wajen Iran kan gwajin makami mai linzami, Araqchi ya ce: Tabbas Iran tana goyon bayan wadannan gwaje-gwajen. Kuma shi kansa ya sha fadin cewa diflomasiyya ta ginu ne a kan madafun iko, kuma ana gina iko ne ta hanyar irin wadannan abubuwan tsaro. Ya kara da cewa yana mai imanin cewa da Iran ba ta da karfin makamai masu linzami, da babu wanda zai yi tunanin gudanar da zaman tataunawa da ita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments