Iran Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Kasar Amurka Joe Biden Dangane Da Hari Kan Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Joe Biden Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Joe Biden

Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewa yayin da yake mayar da martani ga kalaman shugaban kasar Amurka Joe Biden, dangane da masaniyar da Amurka take da shi na cikakken bayani kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran, ya ce duk wanda ke da masaniya kan hakan zai dauki alhakin duk wata barna da harin zai haifar.

Dangane da bayanan da Biden ya yi inda ya yi nuni da cewa ya san lokaci da yanayin harin da yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran, Araqchi ya kara da cewa: Mutumin da yake da ilimi da masaniya kan lokaci da kuma yadda haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai wa Iran hari zai dauki nauyi alhakin duk wata barna da harin zai janyo.

Joe Biden ya ce, a karshen ziyararsa a Berlin a ranar Juma’ar da ta gabata, da kuma jawabin da ya yi wa manema labarai, ya ce: Yana sane da hanya da kuma lokacin da yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran hari, kuma ya ki bayar da karin bayani kan wannan batu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments