A maida martanin jojojin kasar Iran ga hare haren Amurka da HKI a kanta, a yakin Ramadan, sojojin kasar sun yi nasarar lalata ginegine dauke da makamai ko kayakin yaki har 274 a cikin sansanonin sojojin Amurka 24 a yanking abas ta tsakiya, wadanda wasu suka kiyasta cewa gyaransu zai kai dalar Amurka biliyon $15.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran, ya nakalto Mujallar Wall Sreet Journal wacce ta nakalto wani kwarerre a sanin hotunan taurarin dana dam yana fadar haka. Sannan wasu majiyoyin gwamnatin Amurka kanat sun tabbatar da wasu rahotannin.
Ma’aikatar yaki ta Amurka Pentagon ta bada rahoton cewa akalla ana bukatar dala biliyon $5 don sake gina wasu sansanonin, a yayinda wasu suka kai shi hard ala biliyon $15. Wannan ban makamai da kayakin aikin sojoen da aka lalata.
Rahoton ya kara da cewa a cikin makonni biyu kacal da fara yakin Iran ta lalata gine gine har 119 a sansanonin Amurka 13 a yankin. Mafi yawansu a kasar Kuwait, kamar yanda hotunan satlite suka bayyana.
Mujallar ta ce, sojojin Iran sun wargaza rundunar sojojin ruwan Amurka mafi a yakin da ke Bahrain, har sai da Amurka ta dauke sojojinta daga kasar da kuma Kuwait.
Hakama a kasar Jordan sojojin Iran sun lalata sansanonin sojojin Amurka da kuma wuraren taron sojojin Amurka sai da ya kaiga ta daukesu zuwa inda makamai Iran ba zasu je kai ba.