Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kwamitin Tsaro Na MDD Saboda Hare-Haren HKI Kan Kasar

Jakadan JMI a MDD ya kira taron gaggawa na kwamatin tsaro na MDD don tattauna kan hare-haren ta’addancin da HKI ta kai a kan wasu

Jakadan JMI a MDD ya kira taron gaggawa na kwamatin tsaro na MDD don tattauna kan hare-haren ta’addancin da HKI ta kai a kan wasu wurare a nan Iran a safiyar yau Jumma”a.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yada labarai a na kasar Iran na cewa jakadan zai fadawa kwamitin hakkin Iran na maida martani kan wadan nan ayyukan ta’addancin

Amir Said Iravana zai bukaci kwamitin tsaron ya dauki matakan da suka dace kafin al-amura su fita daga yadda suke a halin yanzu, ya kuma shafi  yanking aba daya.

Iravani ya yi allawadai da hare haren da HKI ta kai kan cibiyoyin Nukliyar kasar Iran na zaman lafiya a kasar. Ya kuma kammala da cewa hare-haren da HKI ta kai kan wadannan cibiyoyi ya sabawa dukkan kudurin MDD kuma iran tana da hakkin maida martani da mizanin da ya dace.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi Ya Ce Hare-haren HKI Takalar Yaki Ne Kuma Iran Zata Rana

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted