A cikin wata wasikar mayar da martani da Jakadan kasar Iran na din-din-din a majalisar dinkin duniya ya aikewa da kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya ya karyata zargin da Amaurka da birtaniya suka yi mata na hannun kan abubuwan dake faruwa a tekun bahar maliya da kuma ci gaba da hare haren ramuwa da Kasar Yamen ke kai wa,
Jakadan na kasar Iran Amir Saeid Iravani ya mayar da martani ne game da zargin da kasashen Amurka da Birtaniya suka yi mata a wajen taro da aka yi a ranar 14 ga watan maris, inda ya bayyana cewa wakilan kasashen Amurk da birtaniya sun zargi iran da hannun wajen abin da ke faruwa a tekun bahar maliya kuma ya bayyana zargi a matsayin mara tushe balle madafa,
Haka zalika ya kara da cewa wata dam ace kasashen biyu suke neman fakewa da ita domin cimma manufofinsu na siyasa da kuma halartar matakin da suka dauka na kaddamar da hari kan kasar Yamen day a sabama dokokin diplomasiyya
Ana sa bangaren jakadan kasar faransa a wajen taron ya bayyana cewa babban rashin Adalci ne a jingina irin wannan zargin kan kasar iran , daga karshe iran ta bukaci kasar Faransa a matsayin tan a mamba mai kujerar din din din a kwamitin tsaro da ta yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta na taka burki kan yin zargin karya ga kasahen masu yanci ba tare da wani dalili ba.